Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

LABARU






SANNU DA ZUWA !
MUJALLAR MUDUBI

Tarihi

HOTUNA

LABARU

Adireshi

HANYOYI

Filin Baki

BANGON MUJALLU

FINA-FINAI MASU FITOWA

MU SAN 'YAN WASA

TUNA BAYA

  


LABARAI


MANYAN LABARAI

Fitaccen jarumi Ahamed S. Nuhu ya auri Jaruma Hafsat Shehu. Soyayyar da jaruman biyu suka dade suna zubawa wadda ta zama abar kallo da kwatance a fagen shirin fim na Kannywood. Sai dai kuma a gefe daya, bikin ya zo da matsaloli daban daban wadanda suka kama daga tashin aljanu da kuma uwa uba shigar da Bira'izai suka yi wa angon ba shiri bayan an daura auren. Can gefe daya kuma wajen walimar an ta samun mutane na suma da fita daga hayyacinsu saboda cinkosan jama'a. Ba shiri aka dauko ango ranga-ranga maimakon a shige da shi dakin amaryarsa, sai aka wuce da shi gadon asibiti...

kimanin sama da naira miliyan daya da dubu dari hudu da ashirin aka tara a wurin taron tallafawa masu fama da bala'in yinwa a Jamhuriyar Nijar. Sai dai kuma a wajen gefe daya wasu daga cikin masu shirya taron sun bawa hammata iska da Yakubu Lere da Ahmad Al-Kanawy don jin kadin wadancan kudade na marayu da aka tara a baya. Bikin wanda bai samu amsawar wasu daga cikin 'yan fim an tashi bayan an soki da kuma yin butulci da Mallam Ibrahim Shekarau. Wadannan kudade an kuma fara surutai daga baya kan ya za a yi da su, kuma wanene za a bawa amarsu. Mutane da yawa na jiran lokacin kai su Nijar don bawa wadanda aka yi domin su. Amma har yanzu shiru.... 

An daura auren Jarumi Ibrahim Maishunku da abar kaunarsa Zainab Ahmad Nagi. Soyayyar da suka dade suna yi wa juna sama da shekara 10. Bikin wanda aka yi ittifaki cewa ba a taba yin irin a fagen shirin fim ya kayatu kwarai da gaske. 'Yan fim da dama sun nuna korafinsu kan ta ware da aka nuna masu. Wasu daga cikin mata kuma sun rakashe yanda ba a zato ta hanyar saka muggan kaya da dabi'u na rashin alkinta kai. Da yawa daga cikin wadanda...

 

KANANAN LABARAI

yayin da sana'ar fim ke samar da dubban aikin yi da kudade ga jama'a, baya-bayannan an sami ambaliyar wasu mata da maza a cikin industiri wadanda ta'asar da suke tabkawa ta nuna cewa ba sana'ar fim ce ta dame su ba. Wadannan batagari ba abin da suke illa farautar maza da mata bayan kuma sabuwar akidar shaye-shaye da suka shigo da ita. Kayan mayen sun hada da Roche, Veniline da kuma tabar Wiwi. Baya ga wannan, ga gidaje da aka bude da sunan 'yan fim wanda ake shige da fice da sabbin maza ko mata gajoji..

 Nura Imam, Zainab Idris da Hawwa Musa Katanga sun kai karar kamfanin wayar hannu na v-mobile a babbar kotun Kano inda suke neman hakki bisa ci da guminsu da kamfanin ya yi ba bisa ka'ida ba. MUDUBI ta tattauna da Abbas Sadiq wanda shi ne aka fara tuntuba domin kai 'yan wasa lokacin da za su yi wa kamfanin talla. To ya aka yi V-mobile ya karya yarjejeniya?

Mummunar halayyar nan wadda ta zama annoba a industiri wato 'Kantawaye', za a iya cewa nan ba da dadewa ba za ta zama tarihi. Ita dai wannan kalma ta kantawaye ta samo asali ne daga irin yadda furodusoshi da daraktoci ke yi wa sabbin-shigar sana'ar fim wayo. Wadannan sabbin shiga akwai mata ko matan aure wadanda ke ko kan yi sha'awar yin fim suna kwaso kudi su shigo industiri da nufin za su zama furodusa ko'yan wasa. Wata sabuwar yarinya ta tona asirin wani tsohon furodusa dattijo wanda sunansa ya fara da 'Da' inda ta kwashe labarin yadda suka karke da tsohon furodusan kan niyyarsa ta neman hadin 'kai' daga gareta...

Jama'a da dama sun soki lamirin yadda bikin furodusa Aminu Bala ya gudana. Wannan suka dai ya samo asali ne sakamakon yadda 'yan matan fim da dama suka yi gwangwajewar da ake gani ta zarce mizani. Wani dan fim mai fitowa a matasayin uba wanda ya ce a boye sunansa, ya shaidawa MUDUBI cewa bai dace mutum kamar Aminu Bala ya hada 'picnic' wanda 'yan mata za su yi shigar banza ba. Wata rawa da aka yi a wajen ta janyo cece-kuce a industiri inda wasu da ke kallon abin a gefe suka rika cewa sabbin 'yan mata da ke tururuwar shigowa industiri suna zubar da mutuncin industiri...



....NEMI MUDUBI A YAU !!