Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Tarihi






SANNU DA ZUWA !
MUJALLAR MUDUBI

Tarihi

HOTUNA

LABARU

Adireshi

HANYOYI

Filin Baki

BANGON MUJALLU

FINA-FINAI MASU FITOWA

MU SAN 'YAN WASA

TUNA BAYA

  


Tarihi


Gaskiya Daya Ce...

An fara buga wannan mujalla ta MUDUBI a watan nuwambar shekarar 2003.Tauraron ta na farko shi ne sabon dan wasan nan wato Abba -el mustapha. An kafa ta ne don kawo ci gaba da daukaka harkar shirin fim din Hausa a idon duniya baki daya. 

Bayan ga wannan akwai kyakkyawar niyyar daga martaba da darajar masu fim din Hausa. MUDUBI ba ta fito don muzanta ko muzgunawa wani ko wata dake cikin harkar fim din Hausa ba. Ana buga wannan mujalla a kamfanin Movie World International, f50/51 Shy plaza. Kano,Nijeria. Kuma tana fitowa duk bayan wata biyu. Mun yi tunanin buga ta akan takarda mai leda tare da santsi, don kawo ci gaba ta fannin karatun mujallun fina-finan Hausa, kuma ana buga ta kala gaba daya, sannan farashin da ta fara dashi, shine N 150.00 don ba wa masu karamin karfi dake sha'awar karanta harkar fim dama. 

SHUGABANCI A MUDUBI

MUDUBI ta hada manya da kanana mutane a cikin ta don bada gudummowa ta musamman a bangaren rubutu.Sanan nun malaman dake jami'ar bayero ta kano, na cikin kwamitin musamman masu bada shawara ga wannan mujalla.Bayin Allah'n sun hada da Proff.Abdallah Uba Adamu da Dr. Umar Faruk Jibril. Bayan suma akwai manyan malamai da suke bada tasu gudunmowar ta bangarori da dama. Sannan akwai ma'aikatan gwamnati da kuma yan kasuwa. Ga jerin shugabancin yadda yake...

Mawallafi

Aminu A. Sheriff

Darakta

Bashir A. Sheriff

MASHAWARTA

Proff. Abdallah Uba Adamu

Dr. Umar Farouk Jibril

D.S.P Ibrahim Makama

Alh. Abba Lawan Daneji

Amb. Daudu Suleiman

Barr. Hadiza Adado

C.P. Abdulhadi Zarewa

Edita       --Saudat Kabir

Marubuci na musamman      -Sani Abdulkadir

Tsarawa          -Nura Tijjani Abubakar

Kasuwanci     --Aminu Danpillo

Wakilai         --Abubakar Y. Ladan, Muhd Smart, Muhd Jauro,.

E-mail

Ka/Ki na da niyyar turo mana da shawara ko tambaya? Rubuto ta 


mujallarmudubi@yahoo.com

Web Site

www.mudubi.itgo.com,


Mun Gode, A Je Gaba